Za a kashe wani soja ta hanyar rataya

Wata Kotun sojin sama ta yanke wa wani soji hukuncin kisa bayan ta same shi da laifin kisan budurwarsa wadda ita ma sojin sama ce mai suna  Solape Oladipupo aka Shomzy Shomzy a ranar 12/3/2017 a barikin sojin sama da ke garin Makurdi na jihar Benue.

Kalu Bernard ya bindige masoyiyar tashi ce a cikin dakinta da ke cikin barikin sojin sama na garin Makurdi bayan ya zarge ta da yin  soyayya da wani daban ba shi ba'

Yayin da yake yanke hukuncin jiya,shugaban Kotun sojin Gp. Capt. Elisha Bindul ya sami Bernard da laifi 6 cikin laifuka 8 da aka cajeshi da su a gaban Kotun kuma ya yanke wa Bernard hukuncin kisa ta hanyar ratayewa har sai ya mutu.

Lauya mai kare mai laifin ya ce zai daukaka kara.


Shafin mu na Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120. Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120. Shiga www.isyaku.com Don samun cikakken shafinmu.
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN