Birnin kebbi - An kashe wani matashi da ake zargi da satan babur a Banki

Da misalin karfe 4:15 na yammacin yau Talata dubun wani da ake zargi da satan babur ya cika yayin da ya yi yunkurin satan babur a Bankin KeyStone a cikin garin Birnin kebbi,hakan ya zaburar da matasa da suka harzuka kuma suka rufe shi da duka wasu kuma suna jifarsa da duwatsu.

Wanda ake zargin dai matashi ne da ake zaton  cewa dan garin Gwadangaji ne da ke kusa da Birnin kebbi kuma yana sanye da sutura kamar na ma'aikatan Banki watau bakin Kwat da wando.

Bayanai sun nuna cewa matashin ya sa makulli ne a wani babur kirar roba-roba da niyyar ya tayar da baburdin kwatsam sai ga mai babur na hakika wanda takaddama da ta taso yasa matasa da ke wajen suka afka wa wanda ake zargin da duka lamarin da ya kai ga mutuwarsa bayan 'yan sanda sun kai shi asibiti inda Likita ya tabbatar da mutuwarsa.

A jawabin da Kwamishinan 'yan sanda na jihar Kebbi CP Ibrahim Kabiru yayi wa manema labarai,Kwamishinan ya tabbatar da faruwar lamarin ya kuma kara da cewa "Rundunarsa ta kama fiye da barayin baburra 50 a fadin jihar Kebbi,wasu daga cikin su an yanke masu hukunci yayin da wasu suna jiran a yanke masu hukunci kuma abun takaici shine barayin baburran har kashe masu achaban suke yi  kafin su sace baburran a wajensu"

Ya kara da cewa "Mutane sukan dauki aiwatar da danyen hukuncine saboda sun gaji domin shari'a yakan dauki  dogon lokaci misali wadanda suka saci babur shekaran jiya a yankin Zuru sun shigone daga wata jiha,na jiya kuma da aka kama daga jihar Kaduna suka fito daya kuma daga Kano saboda haka mutane sun gaji da bin tsawon shari'a shi ya sa suke daukan doka a hannunsu kuma wannan ba daidai bane domin laifi ne".

CP Ibrahim Kabiru ya bukaci jama'ar jihar Kebbi da su kasance masu bin doka da oda kuma a kai zukata nesa idan irin wannan lamarin ya faru ba wai a dauki doka a hannu ba.


Ku biyo mu a https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120. Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120. Shiga www.isyaku.com Don samun cikakken shafinmu da ke dauke da ababe masu kayatarwa.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN