• Labaran yau

  An kama 'dan sandan bogi a Kano

  Hukumar 'yan sanda a jihar Kano ta damke wani mutum mai suna Muhammed Yakasai da ake zargin cewa ya shahara wajen damfaran bayin Allah a bisa yin sojan gona cewa shi ko dai jami'in dansanda ne ko ma'aikacin Kotu ne wata hanya da yake amfani da ita domin ya damfari jama'a ta hanyar karban kudi.

  Ranar 27/7/2017 wata mata ta kira sashen kula da cin hanci da tabbatar da da'a na rundunar 'yansanda (Public Complaint Rapid Response Unit PCRRU)a layin su na tarho bayan wani mutum ya karbi kudinta N100,000 da nufin cewa zai sa a bayar da belin danta wadda tun farko sashen yaki da masu fashi da makami na SARS suka kama shi kuma suka gabatar da shi a gaban kotu a bisa zargin aikata laifin fashi da makami.

  Amma bayan Yakasai ya karbi kudin sai ya kasa cika alkawari da ya dauka kuma Alkalin Kotun yasa aka adana wanda ake zargin a gidan yarin Kurmawa da ke cikin birnin Kano.

  Yakasai ya amsa laifinsa a gaban 'yansanda kuma an mayar  wa matar kudinta  da Yakasai ya karba yayin da rundunar ke shirin gabatar da Yakasai a gaban Kotu.
  Ku biyo mu a https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120. Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120. Shiga www.isyaku.com Don samun cikakken shafinmu da ke dauke da ababe masu kayatarwa.
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  Rubuta ra ayin ka

  Item Reviewed: An kama 'dan sandan bogi a Kano Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama