Kwamandan boko haram da ke da hannu a sace 'yan matan Chibok yayi saranda

Bayanai da ke fitowa daga rundunar tsaro ta Najeriya sun nuna cewa wani babban kwamandan kungiyar boko haram da ya taka gagarumar rawa wajen sace 'yan matan Chibok a 2014 Auwal Ismaeela ya yi saranda ta hanyar mika kansa ga rundunar sojan Najeriya.

Auwal Ismaeela yana cikin manyan kwamandodin boko haram guda 100 da rundunar sojin Najeriya ke nema ruwa jallo.

Rahotanni da ke fitowa daga rundunar soji a Abuja sun nuna cewa Auwal Ismaeela yana amsa tambayoyi tare da yin bayani ga masu bincike na rundunar ta soja a Abuja.

Auwal Ismaeela ya amsa cewa yana da hannu a kisan dalibai 20 da aka yi wa wasu dalibai yan makarantar sakandare a Madagali na jihar Borno,kuma yana daya daga cikin babban jami'an leken asiri na kungiyar ta boko haram.

Ya kuma kara da cewa yayi nadama dukkannin abubuwan da ya aikata a can baya domin an rude shi ne cewa hanya ce ta addini amma ya gano cewa ba koyarwar addini ne akeyi a boko haram ba.


Shafin mu na Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120. Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120. Shiga www.isyaku.com Don samun cikakken shafinmu.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN