Yadda raguna suka kara kudi kafin Sallar Layya a kasuwa da kewayen B-kebbi

A kasar Hausa gabanin bukukuwan Sallah karama ko babba abin da za ka kula shine hauhawan farashin kayan masarufi musamman wadda ya zama wajibi ayi amfani da su lokacin bukukuwan Sallah.

ISYAKU.COM yayi  tattaki zuwa kasuwar Kalgo wadda kasuwace da ta shahara musamman bangaren dabbobi wadda ake kawowa daga kauyuka da ke kewaye da garin Kalgo,har da garuruwa kamar Makera ,Bunza,Jega Birnin kebbi,Gulumbe,Diggi Kola da sauransu.

Yayinda muka zagaya kasuwar wadda take ci ranar Alhamis musamman bangaren dabbobi,kasuwa cike take da raguna kowane iri kake so,amma farashi kam sai ka shirya.Domin ragon N30.000  a da sai kana da N50.000 zaka same shi a yanzu,haka zalika idan kana bukatar rago mai matsakaicin kudi ,lallai sai kana da akalla N45.000 ko N50.000 amma idan kana bukatar wadataccen rago ai sai ka shirya N68.000 zuwa fiye da N75.000.

Ko miye ke sa irin wannan tsadar kayan masarufi gabanin kowane bikin Sallah ?


Shafin mu na Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120. Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120. Shiga www.isyaku.com Don samun cikakken shafinmu.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN