Birnin kebbi - An gabatar da mutum 2 a gaban Kotu a bisa zargin aikata Luwadi

Wasu mutum biyu  sun gurfana a gaban Kotun Upper Sharia Court1 da ke garin Birnin kebbi a bisa zargin aikata luwadi.Wadanda ake zargi sun hada da Dahiru Muhammed da Suleiman Maidawo.

Mai gabatar da kara Sgt.Muhammad Auwal ya karanta laifinda ake tuhumar mutanen su biyu a gaban Alkali inda ya karanta wa Kutu cewa wasu 'yan Banga su biyu su ne suka kama Suleiman Maidawo da Dahiru Muhammed  suna aikata luwadi a gonar Alh.Muh'd da karfe 9:30 na daren 29/7/2017.

Alkali Usman Abdullahi S.Kudu ya sake karanta wa wadanda ake tuhumar laifinda ake tuhumarsu da aikatawa watau hada baki domin a aikata laifi sashe na 123 da aikata luwadi sashe na 131 na kundin Penal Code na dokokin jihar Kebbi kuma daga karshe dukkannin mutunen biyu  sun musanta aikata laifin a gaban Kotu.

A bisa wannan dalili ne Alkali Usman Abdullahi ya dage sauraron shara'ar har zuwa mako biyu nan gaba amma ba'a bayar da belin wadanda ake zargin ba. 

Barrister Abubakar Abdullahi daga Shantali Chambers shine Lauyan da ke tsaya wa wadanda ake zargin a gaban Kotu,kuma ya roki Kotu ta bayar da belin wadanda ake zargin kafin ranar da zasu dawo gaban kotu.Ya kuma shaida wa Kotu cewa wadanda ake tuhumar ba zasu tsere ba idan an bayar da su beli.

A nashi bayani mai gabatar da kara Sgt.Muhammed ya bukaci Kotu ta duba ko ya cancanta a bayar da belin ko akasin haka.

Alkali Usman ya dage sauraron karar har ranar Alhamis 17/8/2017 inda ake sa ran mai gabatar da kara ya kawo shaidunsa.


Isyaku  Garba - Birnin kebbiKu biyo mu a
https://www.facebook.com/isyakuweb
Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120.
Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120.
Shiga www.isyaku.com Don samun cikakken shafinmu da ke dauke da ababe masu kayatarwa.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN