Tsananin ruwan sama ya kashe wani saurayi

Tsananin ruwan sama yayi sanadin mutuwar wani saurayi mai suna Izuchukwu a garin Owerri na jihar Imo.Ruwan saman da aka shafe fiye da awa 10 ana tapkawa ya haifar da mamayewan ruwa a kusan ilahirin daukacin  birnin Owerri a ranar Asabar.

Bayanai sun nuna cewa an fara ruwan saman ne tun ranar Asabar da dare har wayewar safiyar Lahadi ana sheka ruwan.

Izuchukwu ya gamu da ajalinsa ne bayan yayi kokarin wucewa ta wani gwata a unguwar Nekede ta Arewa wanda ruwa ya mamaye,cikin rashin sani saurayin yazo wucewa kwatsam sai ya fada cikin gwatan inda kansa ya doki gefen kwalbatin.

Da taimakon wasu mutane da ke kusa da gurin aka garzaya da shi Asibitin FMC na Owerri inda daga bisani Likitoci suka ayyana mutuwarsa.


Ku biyo mu a
https://www.facebook.com/isyakuweb
Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120 zamu aiko maka da Labaran mu kai tsaye.
Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120.
Shiga www.isyaku.com Don samun cikakken shafinmu da ke dauke da ababe masu kayatarwa.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN