Shugaba Buhari ya karbi bakoncin wasu Gwamnoni a London

Shugaba Muhammadu Buhari ya tarbi tawagar wasu Gwamnonin Najeriya da manyan jami'ai da safiyar yau a birnin London.Tawagar ta hada da shugaban jam'iyar APC na kasa John Odigie-Oyegun,Gwamna Rochas Okorocha,da sauransu.

Gwamna Rochas yace shugaba Buhari yana cike da annashuwa da kuzari kana yayi matukar farinciki da ziyarar da tawagar ta kai masa.

Majiyar mu ta labarta mana cewa da yake amsa tambaya dangane da jita-jita da ake yayatawa game da shi sai shugaba Buhari yayi dariya yace "dukkannin wadannan jita-jita karya ne" Bayanai sun nuna cewa shugaba Buhari ya ma tambayi Ministan harkokin sufuri Rotimi Amechi ko yaya harkar sufuri ke tafiya a Najeriya sai shi kuma Ministan yayi wa shugaba Buhari bayani dalla-dalla.

Rochas yace "ziyarar tasu ya tabbatar da cewa masu mugayen kalamai dangane da Buhari ba komai bane face mugayen mutane masu mugun nufi da Allah da kanshi ba zai lamunce masu ba".

Wasu Gwamnoni da ke cikin tawagar sun kunshi  Gwamna Umaru Tanko Al-Makura na Nasarawa; Nasir El-Rufai na Kaduna; da Yahaya Bello na Kogi.Ku biyo mu a
https://www.facebook.com/isyakuweb
Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120 zamu aiko maka da Labaran mu kai tsaye. Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120.
Shiga www.isyaku.com Don samun cikakken shafinmu da ke dauke da ababe masu kayatarwa.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN