Muna bukatar maniyi don tsafi: Namiji mai shigar Mata | isyaku.com

Rundunar 'yansanda ta jihar Benue ta kama wani namiji da ya dade yana shiga irin na mata.Dubun wannan mutum ya cika ne a yayin da yake kokarin raba fada tsakanin wasu karuwai biyu a cikin otal da yake zaune sai al'auransa ya bayyana yayin da aka  cukuikuye juna a Otal din Xima Bar da ke titin Kashim Ibrahim a garin Makurdi lamarin da ya kawo karshen fadan nan take saboda mutane sunyi matukar mamaki.

Hakan ya janyo shigowar 'yansanda cikin lamarin inda sukayi awon  gaba da mutumin haifaffen garin Katsina-Ala,inda yayi karutunsa na boko kuma a garin ne iyayensa suke zaune.

Mutumin ya shaida wa 'yansanda cewa an janyo shi ne zuwa kungiyar ta asiri tun yana Makarantar sakandare sanadin da ya sami kansa a cikin wannan halin ta hanyar kungiyar ta asiri wanda ke dauke da alkawarin cewa zai dinga samo maniyin mazaje da suka sadu da shi saboda bukatu na tsafi ita kuma babban matsafiya ta kungiyar da ake kira "sarauniyar ruwa" zata saka mashi da dukiya na samun kudi har iya karshen rayuwarsa.

Bayanai sun nuna cewa mutumin yayi karuwanci a garuruwa da dama ciki har da Lagos,Calabar,Kaduna,Abuja da Ibadan.Ya kuma kara da cewa ya sadu da akalla mutum 1500 a cikin shekara 5 da ya sami kanshi a cikin wannan lamarin.@isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka sami labaranmu ta Whatsapp ? ka rubuto YES a SMS zuwa 08062543120 zamu aiko maka da Labaran mu kai tsaye kyauta a koda yaushe muka wallafa Labari.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN