Birnin kebbi: Motar daukan kaya ta fadi a randabawul | isyaku.com

Da sanyin safiyar yau Asabar wata motar daukar kaya kirar mitsubishi kanta ta fadi a randabawal na hanyar Majalisa/ Badariya a yayinda direbar motar wanda ya fito daga bangaren Badariya yayi kokarin kauce wa wani dan acaba da ya fito daga bangaren Makerar Gandu, bayanai  suka nuna cewa shi direban ya gan dan acaban  girshi kawai a gaban sa.

Yanayin da ya janyo motar ta buge dan acaban kuma ta je ta fadi gaba kadan daga randabawal ta gefen dama daga gabas.

Dan acaban yananan raye inda ya tsira da yan kwarzuna a jikinsa,yayin da mutanen da ke cikin motar da aka kiyasta cewa kimanin mutum 8 ne duka suka tsira ba tare da raunuka ba.

Wani magidanci da ke zaune a kusa da inda lamarin ya faru kuma baya son a bayyana sunansa ya shaida wa ISYAKU.COM cewa "manyan motoci sun sha fama da lamurra irin na hadurra a wannan randabawal saboda motocin da ke dauko kaya zuwa garin Makera ko jamhuriyar Niger sukan biyo ta wannan randabawal inda tsananin lodin kaya da suke yi yakan janyo su shiga randabawal din da kyar".

Magidancin ya shaida mana cewa ko watan da ya gabata wata motar kanta makare da kaya ita ma ta lalace a tsakiyar randabawal din kuma aka dauki lokaci mai tsawo kafin a jaye motar daga kan titin wanda hakan ya haifar da cinkoso na ababen hawa a wannan hanyar.

Bayanai sun nuna cewa hukumomi na kan bincike akan lamarin a yayin da muka rubuta wannan labarin , yunkurin mu na mu ji ta bakin mai hulda da yawun hukumar 'yansanda na jihar Kebbi yaci tura saboda rashin samun layin wayarsa na salula.@isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka sami labaranmu ta Whatsapp ? ka rubuto YES a SMS zuwa 08062543120 zamu aiko maka da Labaran mu kai tsaye kyauta a koda yaushe muka wallafa Labari.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN