Niger Delta: 'Yan Arewa su fice daga yankin mu kafin 1 ga watan Oktoba | isyaku.com

Hadaddiyar kungiyar masu tayar da kayar baya ta Niger Delta da suka kira kansu  "Coalition of Niger Delta Agitators" sun bukaci duk wani dan Arewa ya fice daga yankin nasu kafin ranar 1 ga watan Octoba na 2017.

Wannan ya biyo bayan wani taro na bazata ne jiya a garin Port Harcourt na jihar Rivers wanda daga karshen taron suka sanar da cewa idan 'yan Arewa basu fice daga yankinsu ba zasu kai hari akan rijiyoyin mai na wasu 'yan Arewa da ke yankin Niger Delta.

Kungiyar ta kuma yi Allah wadai da Gwamnatin tarayya akan abinda ta kira "neman sasantawa da Matasa 'yan Arewa".Kungiyar ta kara da cewa dole ne rijiyoyin mai na 'yan Arewa su koma hannun mutanen Niger Delta.

Kungiyoyin da suka yi hadaka akan wannan lamarin sun hada da "Gen. John Duku (Niger Delta Watchdogs); Gen. Ekpo Ekpo (Niger Delta Volunteers); Gen. Osarolor Nedam (Niger Delta Warriors); Major-Gen. Henry Okon Etete (Niger Delta Peoples Fighters); Major-Gen. Asukwo Henshaw (Bakassi Freedom Fighters); Major-Gen. Ibinabo Horsfall (Niger Delta Movement for Justice); Major-Gen. Duke Emmanson (Niger Delta Fighters Network); Major-Gen. Inibeghe Adams (Niger Delta Freedom Mandate); and Major-Gen. Ibinabo Tariah (Niger Delta Development Network)".
@isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka sami labaranmu ta Whatsapp ? ka rubuto YES a SMS zuwa 08062543120 zamu aiko maka da Labaran mu kai tsaye kyauta a koda yaushe muka wallafa Labari.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN