Labarai a takaice

Akalla mutane 50 sun mutu a wani  mummunar hatsarin mota da ya auku a jihar Kebbi.Bayanai sun nuna cewa hatsarin ya auku ne tsakanin Tsamiya da Bagudo kuma wadanda hatsarin ya rutsa da su galibi 'yan kauyen Tsamiya ne wandanda ke kan hanyar zuwa garin Lagos don kasuwanci.

Tsoho Gwamnan jihar Sokoto Attahiru Bafarawa yace bai goyi bayan bincike da ake yiwa Mai Martaba Sarkin Kano ba.Wannan ya biyo bayan zargi da hukumomi keyi masa da sanya kansa a harkokin siyasa da aikata ba dai dai ba a Masarautar ta Kano.

Gwamnatin tarayya tace 'yan boko haram guda hudu ne ta sako domin ta ceto 'yan matan Chibok 82.

Jam'iyar PDP ta mayar da martani  akan kalaman da Bola Ahmed Tinibu yayi cewa PDP bazata ci koda karamar hukuma daya ba a zaben kananan hukumomi da ake shirin yi a jihar ta Lagos.

Kungiyar kwadago ta kasa tayi barazanar shiga yajin aiki idan Gwamnati batayi komai ba akan albashin ma'aikata.

Cutar Ebola ta sake bulla a jamhuriyar Congo.

Dattawan Arewa sun jinjina wa shugaba Buhari akan bin doka ta hanyar damka amanar kasar nan ga mataimakin shi Yemi Osinbajo.

Wata babban Kotu a jihar Benin ta garkame wani jami'in zabe a bisa zargin almundahana

Haka kuma babban Kotu da ke Abuja ta bayar da belin tsohon Ministan birnin tarayya Bala Muhammed.


@isyakuweb  https://web.facebook.com/isyakuweb


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN