Birnin kebbi: 'Yan Shi'a sun gudanar da Muzahara domin a sako Mal.El-zakzaky

Da yammacin yau Juma'a kungiyar 'Yan uwa Musulmi wanda aka fi sani da Shi'a da ke garin Birnin kebbi suka gudanar da wani tattaki na lumana daga Illela yari wanda ya biyo da su zuwa babban titin Ahmadu Bello kuma suka dakatar da tattakin a babban filin wasa na Haliru Abdu da ke garin Birnin kebbi inda suke neman Gwamnati ta sako jagoransu Sheikh Ibrahim El-zakzaky wanda hukumomi ke ci gaba da tsare shi.

Malam Umar Bello daya daga cikin manyan Malamai na 'Yan uwa Musulmi a Birnin kebbi ya shaida wa ISYAKU.COM cewa "wannan fitowa ba shine na farko ba , yace sunyi wannan tattakin ne domin kira a saki jagoran su Mal.Ibrahim El-zakzaky wanda ake tsare da shi kusan shekara biyu wanda yake Kotu ta bayar da umarni a sake shi kuma a biya shi diyya da shi da mai Dakin sa amma har yanzu ba'a sake shi ba kuma babu wani jawabi da aka yi akan ci gaba da tsare shi."

Malam Umar yayi kira ga Gwamnatin jihar Kebbi akan ta sa baki domin a tabbatar da adalci ta hanyar sako jagoran su Mal.Ibrahim El-zakzaky.Ya kuma kara da cewa jama'a su ji tsoron Allah,domin abubuwan da ake fada na batanci akan su duka za'a hadu gobe Kiyama gaban Allah idan abin da ake fada akan su ba gaskiya bane ta masu fadin hakan zasu sami matsala."Domin maganganun jita-jita da ake cewa mu muka fada ba gaskiya bane,domin mu kanmu bazamu iya fadin irin wadannan kalaman ba".

A ci gaba da jawabin sa har'ila yau,Malam Umar yace "wadanda ke furta irin wadannan kalaman ai sai su fada da dalili da hujja cewa ga wajen da aka fada,hatta ma wasu litattafai da ake rubutawa ba mune ke  rubuta su ba kokuma masu ra'ayi irin namu,makiyan mu ne ke rubuta su kuma sai ace ai munce kaza haka kuma kafofin watsa labarai, ba kafafen mu ne ba, ba kuma a wajen mu ne aka ji ba tunda muna da namu kafofin labarai wanda ba'aji wadannan kalaman daga garesu ba illla makiyan mu ne ke bazawa da farfaganda cewa ai 'yan Shi'a sun ce kaza ai ya kamata duk Musulmi  yaji tsoron Allah".

@isyakuweb  https://web.facebook.com/isyakuwebPost a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN