Boko Haram ta sako 'yan matan Chibok 82

Kungiyar Boko Haram ta sako wasu 'yan matan Chibok guda 82 daga cikin wadanda kungiyra ta sace  baya wani namijin kokari da Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta yi.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa anyi musanyar 'yan matan 82 ne da wasu kwamandodin kungiyar ta Boko Haram da hukumomi ke tsare da su.

Wani babban jami'i  a fadar ta Shugan kasa Abba Kyari shi ne ya tarbi 'yan matan a madadin Shugaba Muhammadu Buhari a filin saukar jiragen sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.

Ana kyautata zato Shugaba Buhari zai gana da su yaran a fagar ta shugaban kasa a yau Lahadi.

Shugaba Buhari ya mika godiyar sa ga Gwamnatin Switziland,Sojojin Najeriya,jami'an tsaro,kungiyar agaji ta Red Cross da sauran kungiyoyin sa kai da suka taimaka har aka cima nassarar wannan lamarin.


@isyakuweb  https://web.facebook.com/isyakuweb

 Kana da labari da kake son mu wallafa? ka gan wani lamari ya faru a gaban idonka da kake son Duniya ta sani? kana da ra'ayi ko shawara zuwa ga Gwamnatin jihar Kebbi ko na tarayya? ka aiko da lamarin ka zuwa birninkebbi080@gmail.com 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN