Gasar Kwallo: Sakaba United ta dauki kofi,ta doke Galadima Jega 2 -1 'yan sanda sun kare kofin kafin a bar filin wasan

An kammala gasar wasan kwallon kafa na jiha ajin Federation cup wanda aka dauki makonni ana bugawa tsakanin kungiyoyin kwallon kafa na jihar Kebbi wanda daga karshe Sakaba United ta yi wa Galadima Jega ci daya mai ban haushi wanda hakan ya bata nassarar lashe kofi.

Tun a rabin lokaci na farko Sakaba United ta zura kwallo a ragar Galadima Jega,bayan da aka dawo rabin lokaci 'yan kwallon Galadima Jega sun taka rawar gani iya burgewa,amma kash basa tare da sa'a a wannan wasan ta yau akan dalilin cewa kusan 'yan wasan sun sami dama har sau 6 da zasu iya rama ci daya da Sakaba united tayi masu amma basu sami sa'a ba.

A nashi jawabi AC Ladan kwamishinan watsa labarai na jihar Kebbi ya shaida wa ISYAKU.COM cewa wannan wasace ta karshe ta Federation cup wanda akeyi kusan ko'ina a fadin Najeriya a wannan mako,yace wasu sun yi jiya wasu yau suke yi dama kowace shekara ana yi kuma can da ana ce mashi challenge cup daga baya aka canja mashi suna zuwa federation cup.

AC Ladan ya kara da cewa wajen kungiyoyin kwallo 14 suka shiga wannan gasa amma gashi yau ana buga kwallon karshe tsakanin Galadima Jega da Sakaba United. Kwamishinan ya nuna irin hazakan da yan kwallon jihar Kebbi ke nunawa ya tabbatar da cewa idan suka sami kyakyawar jagoranci lamarin zai zarce yanda ake zato wajen samun nassara a harkar kwallon kafa a jihar Kebbi.

A ci gaba da bayanin sa AC Ladan yace bukatar masu shirya wasannin da kuma Gwamnati shine maganar ingantaccen filin kwallo da zai yi daidai da zamani wato stadium wanda yake ankai koke tun wancan Gwamnati da wadanda suka wuce Allah yasa ba'a sami biyan bukata ba,amma wannan Gwamna da muka yi mashi magana kwanakin baya yayi na'am da haka ya kuma ce shekarannan za'a fara yin wani abu game da wadannan.Ba wai a nan Birnin kebbi ba kawai,yana son kafin ya kare mulkin sa karo na farko ya kasance yayi stadium babba a Birnin kebbi,kanana a Argungu Yauri da Zuru wannan abin da yayi mana alkawar kenan kuma muna da tabbacin za'ayi hakan ba tare da dadewa ba.

Dan majalisan dokoki na jihar Kebbi mai wakiltar Jega,Gwandu da kuma Aliero Hon Muhammed Umar Jega ya ce kwallon kafa sana'a ce sosai saboda kwallon kafa yanzu a duniya ana karfafa wa matasa gwuiwa kuma Duniya ta sansu kuma u sami jari a ciki.Yace saboda haka yana da kyau wadanda suka kware su nuna kwarewan su domin su wakilci wannan jiha da kuma Najeriya gabadaya.

Daga karshe an mika kofi ga Sakaba United da kyautar kudi N200,000 da kuma kayan wasa a yayin da Galadima Jega ta sami kyautar N100,000 da kayan wasa. Saidai daga bisani wasu da suka harzuka akan cewa Galadima Jega bata ci gasar ba sun tayar da dan takaitaccen husuma inda suka dinga jifa da duwatsu kuma suka yi yunkurin kwace kofin daga hannun 'yan kungiyar Sakaba United,amma kasancewar manyan jami'an Gwamnatin jihar Kebbi kamar su AC Ladan da kwamishina Matasa Hon Maye da kuma jami'an yansanda yasa lamarin ya lafa.

Yan sanda sun kare kofin da 'yan kwallon na Sakaba United da ke rike da kofin inda suka garzaya wajen filin wasan a cikin motarsu a guje.Babu wani rauni ko barna da aka yi wa wani daga bisani dai an watse taro lafiya.

Da ISYAKU.COM ya tuntubi mai horar da 'yan wasa na Galadima Jega Alhassan Muhammed Jega dangane da abin da ya faru,mai horar da yan wasan yace Allah ne bai basu nassara ba a wasan da aka buga ya kuma ce ai su ba baki ne ba a wajen buga wasan kwallo saboda haka abin da zai iya faruwa sun san da shi.Ya kara da cewa sun fi shekara goma sha suna buga wasan ,kaawai da bamu da sa'a ne amma duk dama da muka samu domin mu ci kwallon mun samu amma bamu ci ba,kawai dai bamu da sa'a ne kawai a wannan wasan.Gaskiya wasa abin da alkalin wasa ya hura babu ha'inci a ciki duk hargowa da magoya bayan mu ke yi akan cewa anci amanar mu ba haka bane,kasan shi masoyi bazaka hana shi fadin ra'ayin sa ba.

@isyakuweb  https://web.facebook.com/isyakuweb


 Kana da labari da kake son mu wallafa? ka gan wani lamari ya faru a gaban idonka da kake son Duniya ta sani? kana da ra'ayi ko shawara zuwa ga Gwamnatin jihar Kebbi ko na tarayya? ka aiko da lamarin ka zuwa birninkebbi080@gmail.com 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN