Zargi: Dan sanda ya kwankwadi barasa ya haddasa hatsari da ya kashe mutum 2

Wani mummunar hatsari ya faru tsakanin wasu motoci kirar toyota camry sumfurin 1999 da 2000 da safiyar yau a kan titin Gwarumpa da ke Abuja babban birnin Najeriya.Hatsarin ya rutsa da wani hafsan dan sanda wanda ke sashen SAS da wata mace da ke zaune tare da shi a gaban motan yayin da dan sandan yayi kokarin juyawa  zuwa daya hannun ba tare da la'akari da cewa wata mota tana tafe a gujeba inda ita motar ta afka wa motar da dan sandan ke ciki wanda yayi sanadin mutuwar dan sandan da mace da ke gaban motar dareda shi nan take.

Daily Post ta ruwaito cewa yayin da ake kokarin jire gawakin dan sandan wanda ake zargin yayi tatil da barasa da na yarinyar da ke cikin motar mai lamba KEM 199 NP an gan kimanin kwalaye 10 na kwayoyin tramadol,kwalaben wiski da ba'a shanye ba da dai sauran su.

Jami'an hukumar kiyaye hadurra na kasa FRSC sun iso wajen inda suka dauki gawakin a yayin da shi daya mutumin da hatsarin ya rutsa da shi a daya motar shima aka garzaya da shi zuwa asibiti cikin wani mumunar yanayi.


@isyakuweb  https://web.facebook.com/isyakuweb

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN