Shugaba Trump ya kori Daraktan FBI na Amurka

Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya ce dama yana da niyar koran daraktan Kungiyar Biciken Manyan Lefukan Amurka (FBI) tun kafin aba shi shawarar yin hakan.

A wata hira da ya yi da gidan talabijan din NBC ne dai Trump ya yi jawabi game da korar daraktar FBI James Comey, inda ya ce “na jima ina tunanin korarsa, ko da ma ma’aikatar Shari’a bata bani shawara ba da ma zan kore shi a karshe.” To sai dai bayanin da Fadar White House ta yi na nuna cewa Trump ya kori shi ne bisa ga shawarar ministan shari’a Jeff Sessions da mataimakinsa Rod Rosenstein kadai.

Trump ya ce ya gano cewa ba zai iya yarda da Comey ba sannan Comey zai iya durkusar da FBI inda ya ce domin haka baya nadamar koransa. A lokacin hirartasa da NBC ne Trump ya siffanta Comey da cewa “mutum ne mai riya da nuna cewa ya iya abubuwa.”

Trump ya ce ya sha tattauna wa da Comey kan cewa ya kara hazaka kan yin bincike game da Rasha amma Comey bai kula da batun sosai ba inda Trump ya kara da cewa, “idan har Rasha ta yi wani abu dole mu sani, bai kamata a boye mana ba.”

@isyakuweb  https://web.facebook.com/isyakuweb

Wannan labarin ya fara bayyana a shafin TRT

 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN