Yara 3 suna hannun Allah,Kotu ta jefa Uwayen su a gidan Yari

Wasu yara 3 a garin Lagos 'ya'yan Taofik Aremu da Latifat Aremu sun bar gidansu sakamakon rashin iyayensu a tare da su wannan ya faru ne a saboda iyayen yaran suna gida yari akan zargin laifuka daban daban.

Lamarin ya faru ne bayan jami'an hukumar kiyaye dokokin hanya na jihar Lagos sun kama shi kuma suka gurfanar da shi a gaban kotu inda kotu ta sa aka ajiye shi a gidan yari na Badagry.

A yayin da wannan ke faruwa ita kuma mai dakin nashi Latifat,rahotannin sun ce tayi cacan baki ne da mai gidan da take haya a ciki wanda taso Latifat su bargidan ta duk da yake akwai sauran kudin hayan ta na shekara daya.

Bayan cacan bakin ne ita mai gidan ta kai kara a caji ofis na 'yan sanda da ke Mushin inda suka kai Latifat kotu,bayan sauraron karan kotu kuma ta bada umarni a tsare Latifat a gidan yari na Kiri kiri,bayan ta kasa cika sharuddan beli da aka bayar na N50,000 domin babu wanda zai tsaya mata.

Bayan makwabta sun sami labarin abin da ya faru,sun kai ma Latifa yaran domin ta tafi dasu gidan yari,amma jami'an tsaro basu bari hakan ya faruba inda Latifat ta yanke jiki cikin kuka kana jami'an tsaro suka janye ta daga yaran kuma suka maidata cikin gidan yari.


@isyakuweb  https://web.facebook.com/isyakuweb


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN