Majalisar ta nada wani kwamiti domin ta binciki yadda aka tafiyar da aikin na filin jiragen saman a 2014 kum a ta gabatar da rahotun ta ranar Talata karkashin jagorancin mataimakin kakakin Majalisar dokoki Hon.Muhammed Buhari Aliero wanda ya sami halartar 'yan majalisa 12.
A cikin rahotun ta mai shafi 27 kwamitin ta zargi 'yan kwangilan da yin karin kudin kwangila,kwamitin tace adadin kudin ya kamata ya kasance N8,623,742,038.80 amma sai aka tsawwala kudin zuwa fiye da N10,615,735,704.56.Kamfanonin da binciken ya shafa sun hada da ;CGC Nigeria Limited, Avsatel Communication limited, General Engineering co-ground lighting limited, Strauss corporation limited, High Global Solid resources limited and Wago Global Venture limited.
@isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb