Gwamnan Barno Shettima ya jagoranci tawagan ban hakuri zuwa gida Bukola Saraki akan zancen Ndume

Gwamnan jihar Barno Kashim Shettima ya jagoranci wata tawaga ta sarakuna 'yan siyasa da manyan mutane daga jihar Barno zuwa gidan shugaban kakakin majalisar dattijai Bukola Saraki a daren jiya a gidan shi a Maitama Abuja inda suka roki Bukola Saraki akan ya yafe wa Dan Majalisan Dattawa Ali Ndume da majalisar dattawa ta dakatar da shi a satinnan.

Idan baku manta ba,an sami takun saka ne tsakanin Ndume da Majalisar dattawa akan zargin da jaridar Sahara Reporters ta wallafa a shfinta na yanan gizo inda take zargin Sanata Dino Maleye akan rashin kammala karatun Jami'a, shi kuma Bukola Saraki yana fuskantar zargi akan motar alfarma da yayo oda zuwa Najeriya wanda ake zargin cewa takardun shigowa da ita na bogi ne.Daga bisani bincike ya nuna cewa zarge zargen biyu ba gaskiya bane.

Tun farko Majalisar Dattawa ta nada wani kwamiti wanda yayi bincike akan furucin da Ali Ndume yayi akan cewa a binciki Sanatocin guda biyu Dino da Saraki wanda daga karshe aka same shi da laifin yin furuci da ya janyo cece kuce da harma da zubar da mutuncin 'yan Majalisan na Dattawa.Sakamakon haka ne Majalisar ta dakatar da shi har tsawon wata 6.

A nashi jawabin shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki ya ce zai yi nazari akan bukatun na tawagar domin ganin abin da zai iya zama alhairi ga bangarorin biyu.

@isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN