• Labaran yau

  Amurka tayi barazanar daukan matakin kanta a rikicin kasar Syria

  Wakiliyar kasar Amurka a Majalisan dinkin duniya Nikki Haley  tace idan majalisar ta dinkin duniya ta kasa tabuka komai akan harin guba da aka kai a yankin Idlib da 'yan tawaye ke rike da shi a kasar Syria,hakan zai tilasta wa kasar ta Amurka tayi bagan kanta wajen daukan mataki akan lamarin.

  Wannan barazanar ya biyo bayan rahotanni da hutunan bidiyo ne da kafafen watsa labarai na duniya ke ta nunawa wanda a cikin bidiyon aka nuna yara kanana da suka tagayyara a sanadin fashewar abinda masana ke ganin cewa makami mai guba ne da aka yi amfani da shi a yankin Idlib na 'yan tawaye.

  Wakiliyar tayi Allah wadai da kasar Rasha wadda babban kawar ta kasar Syria ce da rashin tabuka komai ko shawo kan kasar na Syria.Bangarorin biyu da ke fada da juna a kasar ta Syria suna zargin juna da kai harin ha guba a yankin na Idlib.

  @isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  Rubuta ra ayin ka

  Item Reviewed: Amurka tayi barazanar daukan matakin kanta a rikicin kasar Syria Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama