Mutum 3,800 suna dauke da cutar HIV a sansanin 'yan gudun hijira a Borno

Sakamakon wani binciken gwaji da hukumar kare cutuka da suka shafi sida na jihar Borno watau Borno Agency for the Control of HIV/AIDS (BOSACA) ta gudanar ya nuna cewa kimanin mutum 3,800 ne ke dauke da kwayar cuta mai karya garkuwar jiki na HIV a sansanin 'yan gudun hijira da ke Borno.Babban sakataren hukumar Mal.Barkindo Saidu shi ne ya shaida haka,ya kara da cewa gwajin an gudanar da shi ne a bisa rabin kai domin wadanda suka yi gwajin sun kawo kansu ne domin a yi masu gwajin kyauta,mataki da ya shafi gwaji a sansanin 'yan gudun hijira 15 a cikin jihar Borno.

Jaridar Guardian ta labarta cewa Mal.Barkindo ya shaida mata cewa yanzu haka kimanin kashi 2.4 kusan mutum 108,000 ne ake fargaban suna dauke da kwayar cutar mai karya garkuwar jiki a bisa kididdiga na hukumar kidaya ta kasa.

Hakazalika,ya kara da cewa daga watan Janairu zuwa watan Maris na 2017 hukumar ta sami rijistan sababbin wadanda suka kamu da cutar ta HIV,yayin da gwaji da aka yi ya nuna cewa akwai yara 70 da ke dauke da cutar a sansanin 'yan gudun hijiran.Ya kuma ce, gaba daya a jihar an sami karuwan wadanda suka kamu da cutar har mutum 18,101 a cikin lokacin da ake bayani wanda a ciki mutum 9,438 ne kawai suke zuwa Asibiti domin karbar maganin cutar da samun kulawa

 @isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb
.


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN