Yadda Za Ka Yi Amfani Da Kwamfutarka Ka Yi WhatsApp


Wata sa’a rubuta sakonni ko kuma tattaunawa da mutane a wayar hannu na android abu ne da kowa ya sani mai yiwuwa, amma a kowani lokaci rubutu a kan naurar kwamfuta yafi sauki.
Domin haka ya sanya Kamfanin WhatsApp ta fitar da hanyoyi 2 daban-daban da mutum zai iya amfani da sabis din na su a ta kwamfutarsa: wato WhatsApp ta yanar gizo a kwamfurta Windows da OS X.

Abubuwan Da Mutum Ke Bukata Wajen Hada WhatsApp A Kwamfutarsa 

A cewar shafin kamfanin WhatsApp ta yanar gizo, mutum zai iya amfani da sabis din WhatsApp (ta yanaz gizo ko a kan kwamfuta ta App) idan har wayar hannun sa na daya daga cikin wadan nan:
• Wayar Android
• Wayar iPhone 8.1+
• Wayar Windows Phone 8.0 and 8.1
• Wayar Nokia S60, Nokia S40 EVO
• Wayar BlackBerry and BlackBerry 10
Idan har mutum zai yi amfani da WhatsApp a Kwamfutarsa, wayar hannun say a kasance tare da data ko Wi-Fi wajen hadawa. Saboda dandalin na aiki tare sabis din WhatsApp da ke wayar hannu mutum wajen gudunar da aikin.
– Misali, idan mutum zai yi tafiya zuwa wani kasa sannan sabis din waya da ke garin wayar hannun sa, mutum ba zai iya amfani da sabis din WhatsApp a wata waya da ba na sa ba.


Yadda Mutum Zai Saita WhatsApp Ta Yanar Gizo

A farko, zaka saita wayar ka da sabis din WhatsApp ta yanar gizo;
1. Mutun na da daman yin hakan ta kwamfutar ta daya daga cikin wadanda nan hanyoyin daban daban na neman abu ta yanar gizo na Google chrome, Opera, Safari ko Edge, ko kai tsaye mutum tafi zuwa https://web.whatsapp.com

2. Daga nan mutum zai ga hadaddiyar lamba (QR Code) wacce zai tanzance ta hanyar amfani da manhajar WhatsApp da ke kan wayar sa. A karkashin lambar, za a samu bayani dalla dalla game da yadda za a yi hakan. Misali a wayoyin IPhone, idan mutum ya latsa alamar saiti (Settings) zai ga inda aka rubuta ‘WhatsApp Web

3. Bayan mutum ya dauke hoton lambar, daga nan zai iya ganin sakonnin sa da ke kan WhatsApp na shi a wayarsa sannan kuma a Kwamfutarsa.
Sabis din WhatsApp ta kwamfuta shigen daya ne da na waya, sai kawai banbanci kawai shi ne a babban naurar kwamfuta ce. Mutum zai iya amfani da duk wani sabis da ya kan yi amfani da shi a WhatsApp wayarsa ta kwamfuta.


Yadda Mutum Zai Saita App Ta WhatsApp A Kan Kwamfutarsa

Saita app na WhatsApp a kan kwamfuta daya ne da yadda a ke saiti WhatsApp ta yanar gizo, sai dai banbancin kadan ne, – – – mutum sai ya yi downloading sannan kuma sa app din a kan kwamfutarsa.
1. Mutum a farko zai yi downloading app din app sabis din WhatsApp kwamfutarsa na Mac ko Windows daga whatsapp.com/download ta kwamfutarsa.

2. Idan mutum na amfani da kwamfutar Mac ce na Apple sai ya kwance fayil din (unzip file) sannan ya maida da app din WhatsApp zuwa ga fayil na Application.

3. Idan kuma mutum ma amfani da kwamfutar Windows sai mutum ya da fayil din .exe sannan ka sanu damar sanya WhatsApp kwamfutar ka.

4. Idan mutum na da WhatsApp a wayar sa, mutum zai ga QR code din ya fito domin scanning da WhatsApp da ke wayar mutum. A karkashen code din, mutum zai ga umurnin da zai taimaka shi wajen inda zai zaba a kan WhatsApp app din. Misali idan mutum na amfani da wayar iOS, zai danna Saiti sannan ya danna WhatsApp Web

5. Bayan mutum ya gama scanning, mutum zai iya ganin duk sakonnin shi da ke bisa kan WhatsApp ne shi a kan wayar a ta kwamfutarsa. Mutum bai bukatan hada wayar da Wi-Fi kafin yayi aiki a waya, amma sabis WhatsApp kan bada shawaran hadawa da Wi-Fi saboda kada ya ci data sosai.

WhatsApp na kwamfuta shigen daya ne da WhatsApp na waya, mutum zai ya yi downloading iya samun sakonni tare da aiwatar duk wani abu da WhatsApp na waya ke yi.
Bayanai A Kan Tsaro
Idan har mutum ya sanya WhatsApp a kwamfuta ko ya shiga shafin WhatsApp ta yanar gizo duk wani wanda ya ke da damar amfani da kwamfutar mutum zai iya ganin sakonnin ka idan har mutum bai fita daga shafin ba. Idan har kwanfutar mutum na da kariya na password, ba wani babban matsala ba ne. Amma idan har mutum ya yi amfani da WhatsApp ta yanaz gizo a kwamfutar jama’a irin ta cafĂ© ko wurin aiki, yana da kyau mutum ya fita shafin sa na WhatsApp idan ya gama amfani da shi.
Idan mutum ya manta ya fita shafin sa na WhatsApp ta yanaz gizp a kwamfutar da ban a shi ba, ko kuma yana ganin cewa wani ya shiga shafin sa, zai iya fita ta hanyar komawa shafin saita WhatsApp da inda ya yi scanning QR code na sa. Sannan kuma idan har a kan iOS ne zai iya danna Saiti daga nan ya danna WhatsApp Web domin samun biyan bukata.

(Alummata)
@isyakuweb  

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN