Jihar Kebbi ta noma ton 3,000,000 na shinkafa,amma buhu na akan N15000


Gwamnan jihar Kebbi Sen.Atiku Abubakar Baguda ya ce shinkafa ta fi man fetur arziki a Najeriya,BBC ta ruwaito cewa Gwamnan ya shida wa wakilin ta haka ne a garin Lagos.Duk da yake shinkafar ana noma ta sosai a jihar ta Kebbi,amma abin mamaki shine har ila yau shinkafa wadda ake ma lakabi da shinkafar Gwamnati ana saida ta a N15000 farashin buhu daya,an sami sauki daga yadda take a watannin baya a lokacin da ake saidawa a N17000 a kan buhu daya.

Alhaji Bagudu ya ce "sau uku ake noman shinkafa cikin ko wace shekara, kuma idan aka dage, to kasar zata rika sayar wa kasashen Afirka da sauran duniya shinkafar.
Ya yi ikirarin cewa a bana an noma kimanin ton 3,000 000 na shinkafa a jihar ta Kebbi sakamakon hadin gwiwa na masu ruwa da tsaki a ciki da wajen jihar, kuma ana fatan nan gaba adadin zai fi haka".

A nashi bayanin wani magidanci a anguwar Rafin Atiku wanda baya son a fadi sunansa yace ya kamata Gwamnati ta maida hankali domin ta bullo da wani tsari da zai samar da sauki ta hanyar rage farashin shinkafa a bisa yadda take a yanzu a cikin jihar Kebbi da kewaye,tunda dai jihar Kebbi tana daya daga cikin jihohi da aka fi noman shinkafa a Najeriya.Saboda haka ya kamata masu amfani da shinkafar su sami wani rangwame daga Gwamnati akan farashin da ake saidawa a kasuwa a cikin jihar Kebbi.

Isyaku Garba   @isyakuweb   ku biyo mu a Facebook

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN