• Labaran yau

  Shugaba Buhari, "mai yiwuwa zan sake komawa Asibiti"
  Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce yana murmure wa ta hanyar samun sauki daga rashin lafiyar da ke damun sa,amma ya ce “ watakila nan da makonni kadan zan sake komawa Asibiti”

  Ya bayyana haka ne a jawabin da ya yi wa ‘yan kasar a fadar sa da ke Abuja jim kadan bayan saukar sa daga birnin London, inda ya kwashe kusan wata biyu yana hutu da kuma jinya.

  A cewar sa, bai taba kwantawa rashin lafiya irin wacce yake fama da ita yanzu ba.

  Shugaba Buhari ya kara da cewa, “Ina matukar nuna godiya ga dukkan ‘yan Najeriya, Musulmi da Kirista, wadanda suka yi ta yi min addu’a, kuma suke ci gaba da yi min addu’ar samun sauki”.

  Shugaba Buhari ya ce yanzu ba a bin da zai sanya a gaba illa ya yi ma ‘yan Najeriya aiki tukuru da gaskiya domin samun rayuwa mai ma’ana a Najeriya wanda ta hakan ne zai nuna masu jin dadi da yayi saboda Addu’a da suka yi ta yi masa.

  @isyakuweb

  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  Rubuta ra ayin ka

  Item Reviewed: Shugaba Buhari, "mai yiwuwa zan sake komawa Asibiti" Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama