Hari kan 'yan Najeriya a Afrika ta kudu

Rahotanni daga kafafen labaru musamman na Najeriya sun yi bayanin yadda wasu batagari 'yan kasar Afrika ta kudu ke kai harin kin jinin baki a kasar, musamman kan 'yan Najeriya mazauna kasar ta Africa ta kudu.wannan al'amari ya zama maimaici kenan kan irin wannan harin da aka yi ta kai wa akan 'yan Najeriya a baya,a wancan lokacin shugaban kasar ta Africa ta kudu Mr Jecob Zuma ya nemi gafara daga Najeriya.

Yanzu kuma,tarihi ya sake maimata kan shi,dalilin da ya sa aka sami wannan maimacin shi ne rashin daukar mataki akan wa'yanda suka kai hare hare akan 'yan Najeriyan a karo na farko ba'a kama kowa ba balle a hukunta shi.Wannan karon kowa surutu kawai ake yi amma su kungiyar dalibai na Najeriya NANS karkashin jagorancin shugaban ta na kasa Kadiri Aruna,ya baiyana wa Jami'an kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN a ofishin DSTV da ke Wuse2 a babban birnin Najeriya Abuja cewa wannan karon dole ne su dau mataki.

Ya kuma ce a madadin sauran daliban Najeriya,sun ba Kamfanonin Kasar Afrika ta kudu awa 48 su fice daga Najeriya ko su gamu da tarzoma na bijirewar Dalibai ta hanyar kai hari domin lalata karafan da ke dauke da na'urorin sadarwar wayar salula (mast) na MTN wanda kamfanin kasar Afrika ta kudu ne,ya kara da cewa  kamfanin DSTV da SHOPRITE basu tsira ba domin duk kamfanin Afrika ta kudu ne.

Idan baku manta ba,Najeriya ta taimaka wa kasar Afrika ta kudu a shekaru na 1988-1990 a lokacin da suke shan bakar wahala da wulakanci a hannun turawa 'yan wariyar launin fata.A dole Gwamnatin mulkin soja karkashin jagorancin Janar Ibrahim Badamasi Babangida ta zabbare wani kaso daga albashin duk wani dan Najeriya da ke karbar albashin Gwamnati aka harhada aka bai wa kasar ta Africa ta kudu.Wadannan kudade sune suka samar da sinadarin rura zafin tafiyar tsarin kyama da fada da tsarin zalunci da bakaken fatar kasar ta Afrika ta kudu ke fuskanta a wancan lokacin kuma a cikin wannan tafiyar suka sami 'yanci.

Ya zuwa yanzu dai ana harsashen cewa akwai yan Najeriya kimanin 800,000 da ke zaune a kasar Afrika ta kudu,wanda kashi 60 na wannan adadin Inyamirai ne da 'yan Niger Delta na Najeriya.

Isyaku Garba -Birnin kebbi

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN