Header Ads

Birnin kebbi- An gudanar da taron Addu'a don Buhari

A yau Alhamis a babban Masallacin Idi da ke anguwar Gesse da ke garin Birnin kebbi ake gudanar da taron addu'a domin Allah ya ba shugaban kasa Muhammadu Buhari lafiya,wanda ya sami halartar mutane da dama.

Wasu Malamai sun sami damar gabatar da addu'a domin Allah ya ba shugaban kasa lafiya ya kuma kiyaye Najeriya,kuma don tattalin arzikin kasar nan ya inganta.

Wannan addu'ar ta Birnin kebbi ya biyo bayan addu'oi ne da aka yi ta gabatarwa a wasu Jihohin Arewacin Najeriya wanda Jihar Borno ta fara gabatarwa kafin wasu Jihohin su dau hannu.
Allah ka ba Kasar mu Najeriya zaman lafiya da kwanciyar hankali,ka bamu,da shugaban Kasa Muhammadu Buhari lafiya.

Powered by Blogger.