Header Ads

Ya bayyana: Guba ne aka sanya wa Buhari,DSS ta gano ko su waye

Bayanai sun nuna cewa akwai gungun wasu mugayen mutane ne da suka tasara cutar da shugaba Muhammadu Buhari ta hanyar guba.Wani Edita kuma marubuci na shafin nan na yanan gizo ta DENISAURUS ya ruwaito cewa idan baku manta ba,ranar Alhamis 19/1/2017 shugaba Buhari ya rubuta wa Majalisa takardar neman hutu na kwanaki 10,ba da dadewa ba kawai sai aka garzaya da shi zuwa kasar Ingila da gaggawa

A cewar Mat Eli Edita na Denisaurus,wata majiya kwakkwara daga Fadar ta shugaban Kasa ta ce sakamakon gwajin da likitoci suka yi wa shugaba Buhari ya fito,kuma babu wani abun tsoro a sakamakon,
da yake Buhari yana nan lafiya,amma ba a sani ba ko guban ya yi wa wasu sassa na jikin shi illa kawo yanzu.Ya kara da cewa wannan bayanin ya zo masu ne kwanaki kadan kafin Ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan harkar tsaro NSA ya yanke shawara akan dakatar da Kwamitin bincike a kan kudin Makamai da shugaban kasa Buhari ya kafa.

FITAR GAGGAWA

A ci gaba da bayani,shafin na Denisaurus yace an shirya Buhari zai bar Najeriya zuwa Ingila ranar Juma'a 20/1/2017 amma saboda tsananin radadin gubar,ya zama dole aka yi fitar gaggawa zuwa Ingila ranar Alhamis 19/1/2017.Idan kun tuna,a daidai lokacin da Shugaba Buhari ya bar Najeriya,mataimakin shugaban kasa Yomi Osinbanjo yana Davos wajen ziyaran aiki,barin shugaban kasa ba tare da kasancewar wanda zai mika wa mulki ba cikin gaggawa kafin Mataimaki Osinbanjo ya dawo Najeriya ya nuna irin tsanani da gubar yayi,sakamakon aikin mugayen Mutane makiya Allah da kin talakan Najeriya.

Bayan isar shugaba Buhari a Ingila inda ya fara jinya,wata jarida ta ruwaito cewa shugaba Buhari ya mutu,wai ya kashe kanshi ne,haba jama'a....sakamakon wannan rashin dattaku da mutunci daga masu tafiyar da wanan jarida,hakan ya tayar wa miliyoyin 'yan Najeriya da masoyan Najeriya hankali.Ma'ana ya zama ala tilas wannan bawan Allah ya nuna wa Duniya cewa yana raye,kenan ba'a son ya sami hutu balle yayi jinya da ya inganta.Bincike ya nuna cewa wannan jaridar an yi mata rijista ne a Arizona na kasar Amurka.

Rahoton ya kara da cewa shugaban hukumar ayyukan asiri da tsaro ta DSS ta kasa Lawal Musa Daura, wani baban aminin shugaba Buhari ne,kuma sun fito daga gari daya,garin Daura.A cewar wani tsohon babban jami'in leken asiri wanda ya san yadda al'amurra ke tafiya,ya ce Lawal Daura mutum ne haziki kuma mai gaskiya wanda babu yadda za'ayi ya ci amanar shugaba Buhari balle ya bari a ci amanar Buhari ko gwamnatin ta Buhari.Tuni dai ma'aikatar ta ayyukan asiri da tsaro suka dukufa domin dakile duk wata hanya da makiya Najeriya ke kullawa domin kawar da Gwamnatin tsabta,gaskiya ,mutunci da amana ta shugaba Buhari.

Isyaku Garba - Birnin kebbi
@ISYAKUWEB


Powered by Blogger.