'YAR KUNAR BAKIN WAKE MAI SHEKARU 10 A DUNIYA TA KASHE KAN TA A MAIDUGURI

A wata karamar yarinya yar kunar bakin wake mai shekaru 10 ta kashe kanta a wani yinkurin harin da ta kai  a birnin Maiduguri dake  arewa maso gabashin Najeriya.
A cewar shaidu yarinyar ta tarwatsa damarar Bam din dake jikinta ne yan mitoci kafin a isa inda aka yi niyar kai harin.
Nan take dai ta rasa ranta, a yayinda  kuma wani mutum guda ya yi mummunan rauni sakamakon tartsatsin fashewar da ta wakana.
yanzu haka dai,  jami'an tsaro na ci gaba da gargadin mutane domin su kara lura tare da zura ido   kan irin wadannan yan kunar bakin waken, da suka bazu  lura da yadda aka tarwatsa sansaninsu dake dajin sambisa.
RFI HAUSA

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN