• Labaran yau

  MARTANIN 'YAN SHI'A GA SAKON BUHARI NA SABUWAR SHEKARA

  Magoya bayan Ibrahim Zakzaki a Najeriya sun mayarwa shugaba Muhammadu Buhari da martani bayan a cikin sakon shi na sabuwar ya bukaci mabiyan na Shi’a su rungumi zaman lafiya tare da bin dokokin kasa.
  A sakon da ya aike wa al’ummar kasar dangane da shiga sabuwar shekara ta 2017 shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bukaci mabiya Shi’a da kuma wadanda ke dauke da makamai a yankin Niger Delta da su rungumi zaman lafiya, sannan kuma su kasance masu mutunta dokokin kasar.
  Amma Ibrahim Musa Kakakin ‘yan Shi’ar a Najeriya, ya ce dama su mutane ne masu kaunar zaman lafiya.
  "Duk da kisan da aka yi wa mutanenmu amma ba mu dauki doka a hannunmu ba, muna ci gaba da bin hanyoyi na lamama". a cewar Ibrahim Musa Al Mizan.
  ‘Yan Shi’ar sun ce Shugaba Buhari ne suke bukatar ya kasance mai bin doka da oda bayan Kotu ta bayar da umurnin a saki jagoransu.
  (RFI )
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  Rubuta ra ayin ka

  Item Reviewed: MARTANIN 'YAN SHI'A GA SAKON BUHARI NA SABUWAR SHEKARA Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama