MAULUDI NABIYU A GARIN BIRNIN-KEBBIDaga Haruna Aliyu Usman- Birnin kebb.-Mutanen Jihar kabi a
Hedikwatan Birnin kebbi sun wayi gari da taro wanda ya dauki hankali,koda
suka bincika 'yan Darikar Tijaniyya ne suka fito cikin daruruwan su
domin nuna murna da haihuwar Mazon Rahma watau Annabi Muhammadu
sallalahu alaihi wasalam.Masu zagayawan sun kunshi matan aure, budare. da kuma yara.Zagayen na awa uku ya samu halartar manyan Shehunnan darikar Tijjaniyya.
Daga bisani aka fara raye-raye domin nuna murna.Duk zawiyyon dake cikin birnin Jaha sun halarci taron.Daga karshe khalifan Ahmad Usman Muktar ya gaya wa manema labarai cewa suna maulidin ne akan hujja ba.a jahilce ba, Khalifan ya kara da cewa Annabi ne yace suyi Mauludi domin nuna soyya a agare shi da iyalan gidan sa.Shugaban ya mika godiyar sa ga mabiya Darikar inda yayi kira ga jama'a da su so Annabi da gaskiya.Daga karshe ya gode ma gwamnatin jaha domin kaso da ta bayar lokacin bukukuwan.
A daga bisani aka wacika da kade kade da raye


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN