Kamar yadda shugaban kasar
Najeriya, Muhammadu Buhari ya cika shekaru 74 a yau, Asabar 17 ga watan
Disamba 2016. Nasarar da yayi a zaben 2015, ya kasance na farko a
tarihin Najeriya shugaban kasa mai ci ya fadi zabe ga dan takarar
jam’iyyar adawa a zaben shugabancin kasa.
Duk
da kalubalan da ya fuskanta a lokacin mulkin soja, soyayyarsa ga kasar
ya kuma basa daman shugabantar kasar a gwamnatin demokradiya.
Ya yinda yake murnar cika shekaru 74, ga abubuwa guda 6 da ya kamata ka sani game da shi.
1. Matsayinsa a ahlin gidansu
An
haifi shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari a ranar 17 ga watan
Disamba, shekarar 1942, a Daura, jihar Katsina. Buhari ya kasance da na
ashirin da uku (23rd) ga mahaifinsa Adamu.
Ya taso a hannun uwarsa Zulaihat kadai saboda mahaifinsa ya rasu yana dan yaro karami.
2. Tashin sa
Mahaifinsa
ya rasu lokacin yana da kimanin shekaru hudu a duniya. Buhari ya taso a
hannun mahaifiyarsa Zulaihat tare da taimakon Mamman Daura da kuma yan
uwansa. Ya halarci makarantar firamare a Daura da Mai’adua.
3. Aikinsa na soja
Ya
shiga aikin soja yana da shekaru 19 a duniya, bayan yay i makarantar
horon sojoji wato Nigerian Military Training College (NMTC) a 1961.
Kasancewar
sa a cikin juyin mulkin soja na Disamba 1983, wanda ya sauke shugaban
kasar demokradiya Shehu Shagari, Buhari yay i aiki a matsayin shugaban
kasa a mulkin soja daga 1983 zuwa 1985.
4. Ka’idodin sa
Buhari ya kasance mutun mai nuna gaskiya da kuma bin ka’idar kashe kudade, wannan ne yasa ya saka fifiko kan yaki da rashawa.
Tsakanin
watanni 20 a matsayin shugaban kasa, an tura kimanin yan siyasa 500,
jami’ai da kuma yan kasuwa gidan yari saboda rashawa. An saki wadanda
aka tsaren bayan sun saki kudade ga gwamnati da kuma yarjejeniyar cike
wasu ka’idodi.
5. Iyalansa
Buhari
ya auri matarsa ta farko, Safinatu yana da shekaru 29 a 1971. Safinatu
ta kuma kasance matar shugaban kasar Najeriya daga Disamba 1983 zuwa
Augusta 1985.
Sun haifi yaya biyar tare, mata hudu da namiji daya. Sun sanya wa yarsu ta fari, Zulaihat wato ta ci sunan mahaifiyar Buhari.
Bayan sun rabu da Safinatu a 1988, ya auri matarsa ta biyu kuma matarsa a yanzu Aisha Buhari a Disamba 1989.
Har ila yau sun samu yara biyar tare, namiji daya mata hudu. Sune Aisha, Halima, Yusuf, Zahra da kuma Amina.
6. Rashin sa
Buhari
ya dandani zafin rashi tun yana dan yaro, idan kun tuna, ya rasa
mahaifinsa yana da karancin shekaru, yayinda mahaifiyarsa ta rasu, yana
cikin tsakanin karshen 40s.
Safinatu Buhari,
matsarsa da suka rabu ta rasu bayan kamuwa da ciwon suga haka kuma yarsa
ta farko, Zulaihat ta rasu sakamakon cutar sikila, jim kadan bayan ta
haihu a Nuwamba 2012, a wani asibiti a Kaduna. Har ila yau ya rasa dansa
Musa, daga aurensa na farko.
Duk da wannan dubin rashi da yayi a baya ya zamo mutun mafi karfi a Najeriya.
Muna taya shi murnar zagayowar ranar haihuwar sa!
Daga Naij.com Hausa
Gida - Leadership Hausa
Assalamu alaikum, Editan LEADERSHIP Hausa mai farin jini, ka bani dama na yi kira ga gwamna Kashim...
Gida
(null)
Labarai, kai tsaye- Radio France Internationale RFI
Samu dukkanin shirye-shiryen RFI Siyasa da Al'adu da Wasanni da Labarai da dumi-duminsu na Afrika da Faransa da duniya.
NIGERIAN NEWSPAPERS
Flash or unlock your phone at SENIORA TECH shop No.51 upstairs.OLUMBO shopping complex Ahmadu Bello way Birnin kebbi. 08062543120 http://...
Wasanni
Domin samun labaran wasanni kai tsaye daga club na kwallon kafa na turai
Tags:
TARIHI