Dokar ta baci kan abinci


Shugaban kasa Bola Tinubu ya sa dokar ta baci kan abinci da ruwan sha don taimakawa rage radadin cire tallafin Mai don haka za a ba mutane milyan 15 tallafin dubu takwas cikin kusan milyan 150 da aka ce sun abka a  mummunan talauci. 

Ga abinci ba kudin Saya mutane masu kudi suna bin kasuwanni suna sayan gero da dawa da shinkafa da masara da wake suna loda manyan motoci suna kaiwa kudu da wajen kasa. Alamu sun nuna yunwa za ta yi barna idan gwamnati ta doge kan cire tallafin Mai. 

Ina dalilin da ita gwamnati ba za ta gyara matatun manta ta rika tacewa ba don farashin ya sauka. Gwamnati ta gwammace yan Nigeria su mutu da yunwa kenan saboda wasu tsirarin da ke amfana da tallafin mai shin sun fi karfin gwamnati ne. 

Me yasa gwamnati baza ta rike tallafin ba ita ta ci moriyarsa ta taimaki mutanen ta. Shin lokacin shugaban kasa Yar Adua babu tallafin ne ya rage farashin mai. Idan sun dage kan wannan raayi su sani Sarkin yawa ya fi Sarkin karfi suna gani kujerar mulki zata musu zafi. 

Komai zai iya faruwa saboda matsalar mai kadai ta lalata kowace hidimar rayuwa don son zuciyar mutane kalilan. Mutane ba za su zauna suna kallo yunwa ta kashe su ba a kasa mai arzikin manfetir ta farko a Afirka cikin kungiyar OPEC. 

Mu ci gaba da adduah Allah ya kawo mafita a ruwan sanyi. 08062333065

Daga Muazu Hardawa Bauchi.

Published by isyaku.com

4 Comments

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

  1. 8k ce zatai maganin talauci a Nigeria, me talaka zai saya da dubu takwas din

    ReplyDelete
  2. Zancen banza a cikin mutum miliyan fiye da 200 za a ba mutum miliyan 12 N8000 hmn.. A bude boda kawai a shigo da kayan abinci da na masarufi har dama fetur tunda an cire tallafi a Najeriya.

    ReplyDelete
  3. Kai jama'a Allah ya isa talakan Najeriya ya gama rasa gata hannun miyagun Yan siyasa

    ReplyDelete
  4. Meye dubu takwas zasuyi da yini kana kashe fiye da dubu takwas

    ReplyDelete
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN