Jerin sunaye: Gwamna Idris na Kebbi ya nada perm sec 2, ya amince da tura saura zuwa ma'aikatu

Kebbi state Governor Dr Nasir Idris Kauran Gwandu

Gwamnan jihar Kebbi Dr. Nasir Idris Kauran Gwandu ya amince da nadin Dakta Shehu Nuhu Koko na karamar hukumar Koko Besse a matsayin sabon Sakatare na dindindin.

 Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban ma’aikata na jihar Kebbi, Alhaji Safiyanu Garba Bena wanda aka rabawa manema labarai a Birnin Kebbi ranar Litinin. Mai taimaka wa Gwamnan Kebbi kan harkar watsa labarai Yahaya Sarki ya sanar da haka a takarda da ya fitar.

 An kuma tura sabon wanda aka nada zuwa ma'aikatar lafiya.

 A cewar sanarwar, Gwamna Idris ya kuma amince da nadin mukaman sakatarorin dindindin a jihar.

 Wadanda lamarin ya shafa sun hada da Muhammad Sani Umar Ma’aikatar Kananan Hukumomi, Garba Umar Dutsinmare, Ma’aikatar Kudi, Aisha Usman, Ma’aikatar Kasafin Kudi, Zaki Dahiru, Al’amuran Gwamnati, Aliyu Mustapha Gwandu, Gidan Gwamnatin Kebbi, Joel Aiki, Ma’aikatar Gona  da Kabiru Aliyu, SAN, ma’aikatar shari’a.

 Sauran sun hada da: Aishatu M. Maikurata, Ministry of Women, Ahmad Yarima, Ministry of Business , Kudirat Shuaibu Diri , Ministry of Environment, da kuma Ibrahim Umar, Ma'aikatar Albarkatun Ruwa.

 Sauran sun hada da Mustapha Abubakar Tata, Sashen Harkokin Protocol, Suleiman Sani Augie, General Administration, Saidu Buhari Warah, Ma’aikatar Yada Labarai, Aliyu Labaran, Sashen Ayyuka na Musamman da Abubakar Ahmed, Ma’aikatar Filaye.

Takarda ta ce wannan sauyin ya fara aiki nan take kuma mikawa da karbar ragamar shugabanci na ma'aikatu wajibi ne a gudanar da shi ranar, ko kafin ranar 14 ga watan Yuni.

1 Comments

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN