Yadda dan siyasar 4+4 ya kunduma ma Sani Zauro Hukuma ashar don BBSO

Da tsakiyar ranar Talata ne wasu matasa suka kai farmaki a gidan P.A na Gwamnan jihar Kebbi Faruku Enabo suka farfasa gilasan wasu motoci da suka samu a kofar gidan.Haka zalika matasan sun kai farmaki a ofishin BBSO da ke Gwadangaji da gidan man Texaco a garin Birnin kebbi inda suka aikata barna ga dukiya tare da taba lafiyar wasu matasa a ofishin na Texaco.

Wata majiya ta labarta mana cewa matasan da ke tafe a cikin motoci guda biyu dauke da adduna suna rera wakokin ashar sun zagaya garin kafin labarin faruwar lamarin ya bulla.

Amma rahotanni da muka samu sun nuna cewa Faruku Enabo ya bukaci kada duk wani masoyinsa ya mayar da martani ko ya nemi daukar fansa.

A nashi bayani, Alh Sani Hukuma Zannan Gwandu cewa ya yi wani babban dan siyasa bangaren 4+4 ya ci zarafinsa ta hanyar zagi, domin kawai an yi ma gidan mai wanda mallakinsa ne a garin Zauro fenti na BBSO.

Zanna ya kara da cewa "shi wannan dan  siyasa ya zagi gwamna Adamu Aliero lokacin da yake gwamna, ya zagi Sa'idu Dakingari shi ma lokacin da yake gwamna haka zalika ya zagi Atiku Bagudu lokacin da yake Sanata saboda haka ni ba zan rama ba domin na san darajar iyaye na sakamakon haka ba zan zagi iyayen wani ba.

Ni a nawa fahimta, da 4+4 da BBCO duka abu daya ake ma aiki watau ganin cewa Buhari da Bagudu sun sake cin zabe na 2019.

Bisa wannan dalili yanzu ya bayyana karara cewa akwai masu zagon kasa ga Mai girma Gwamna Atiku Bagudu, kuma yanzu haka ya fara gane irin wadannan mutane .Kuma muna rokon Allah ya kare shi daga sharrin su.

Rarraba kan jama'armu ba alhairi bane ga siyasarmu, P.A Enabo ne ya yi namijin kokarin ganin cewa ya lallashi yan PDP suka dawo APC a jihar Kebbi.Sakamakon haka ya kamata a tsaya a yi nazari kafin a aikata abu, jama'a muke nema ba fitina ko rarraba ba a siyasarmu ta yanzu a jihar Kebbi".

Daga Isyaku Garba

Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN