Wani bayani da ke da nasSaba da 'yansanda ya ce, lamarin ya faru ne jiya , bayan wani dan acaba ya dauko wani mutum da wata babbar jaka, amma bayan 'yansanda sun tsayar da shi domin bincike, marmakin ya tsaya, sai ya kara wa babur wuta.
Garin tsere wa binciken 'yansanda, sai ya fadi a wani rami, sakamakon haka ya mutu, mai babbar jaka kuma ya yi batan dabo daga wajen sakamakon rudani da ya auku.
Bisa wannan dalili ne washegari 'yan acaba kimanin 3000 suka shiga zanga-zanga da ya kai ga yunkurin kone ofishin 'yansanda tare da kone motar ta 'yansanda.
Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Tags:
LABARI