Kotu ta saki yan boko haram 2 sakamakon rashin gabatar da shaidu

Wata babban Kotun tarayya a Abuja ta saki wasu mutum biyu da aka gurfanar a gabanta bisa zargin kasancewa yan kungiyar boko haram shekara biyar da suka wuce.Wadanda aka saki sune Ibrahim Ahmed da Sani Argungu.

Mai shari'a Justice Binta Nyako ta ce Kotu ta saki wadanda ake tuhuma ne sakamakon gazawar masu shigar da kara na gwamnatin tarayya su gabatar mata da shaidu a kan mutanen ganin cewa wadanda ake tuhuma suna tsare tun 2012.

Justice Nyako ta bukaci wadanda aka sake kada su yi cudani da bata gari kuma za'a sa ido akan harkokin su. Haka zalika ta ce a duk lokacin da masu gabatar da kara suka gama hada shaidu za su iya sake gabatar da su domin a ci gaba da shari'ar.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Kotu ta saki yan boko haram 2 sakamakon rashin gabatar da shaidu Kotu ta saki yan boko haram 2 sakamakon rashin gabatar da shaidu Reviewed by on April 13, 2018 Rating: 5

ISYAKU TV

SANARWA

Seniora Tech tana sanar da jama'a cewa ta koma TAUSHI PLAZA shago mai lamba 50 a hawa na sama yamma da gidan Wazirin Gwandu. Ahmadu Belloy way,Birnin kebbi, jihar Kebbi.
Tuntube mu domin Flashing, cire security na waya ko neman sani game da yanar gizo da sauransu.
Ko ka kira 08087645001
Powered by Blogger.