Dalilin da ya sa na ce a yi wa shugaba Buhari ruwan duwatsu - Toni Momoh

Wani tsohon Ministan watsa labarai a Najeriya Prince Toni Momoh ya yi bayani a kan dalilin da ya sa ya ce yan Najeriya su jefi Gwamnatin shugaba Buhari da duwatsu matukar ya gaza a shugabanci.

Momoh ya yi wannan jawabi ne yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zaben 2015, inda ya bukaci yan Najeriya su jefi gwamnatin APC idan ta kasa.

Ministan ya shaida wa The Sun cewa tuni yan Najeriya suka dade suna jifar shugaba Buhari duk da nassarori da Gwamnatin Buhari ta samu a fannen tsaro musamman ya yankin Borno.

Ya kuma ce a matsayinsa na Minista ya gaya wa jama'a abin da suke son su ji ya kuma rage su da kansu su auna yadda zasu yi da labari da aka ba su.

"Tuni wadansu mutane suna jifar mu, amma wadanda ke wannan jifa yan adawa ne da idonsu ya rufe da  suka gaza ganin nassarori da wannan Gwamnatin ta samu a sassa daban-daban a kasarnan".

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Dalilin da ya sa na ce a yi wa shugaba Buhari ruwan duwatsu - Toni Momoh Dalilin da ya sa na ce a yi wa shugaba Buhari ruwan duwatsu - Toni Momoh Reviewed by on April 15, 2018 Rating: 5

ISYAKU TV

SANARWA

Seniora Tech tana sanar da jama'a cewa ta koma TAUSHI PLAZA shago mai lamba 50 a hawa na sama yamma da gidan Wazirin Gwandu. Ahmadu Belloy way,Birnin kebbi, jihar Kebbi.
Tuntube mu domin Flashing, cire security na waya ko neman sani game da yanar gizo da sauransu.
Ko ka kira 08087645001
Powered by Blogger.