Shugaban karamar hukumar Zuru ya gode wa Gwamna Bagudu kan rijiyoyin burtsatse

Shugaban karamar hukumar mulki ta Zuru a kudancin jihar Kebbi Alh. Muhammed Abubakar Kabir a madadin 'yan majalisarsa da al'umman karamar hukumar Zuru ya mika godiyarsa ga Gwamnan jihar Kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu bisa aminciwa tare da sa hannunu domin gina rijiyoyin burtsatse guda shida a cikin karamar hukumar Zuru.

Shugaban ya bayyana farin cikinsa ga Mai girma Gwamna ganin cewa wannan aikin ya zo daidai lokaci da ya kamata domin shigowar yanayin zafi wanda zai haifar da bukatar ruwa domin amfanin jama'a.

Kansila mai wakiltar Mazabar Senchi Hon.Amina Zama ,shugaban jam'iyar APC na mazabar Senchi tare da manbobin kamfanin da ke yin rijiyoyin na daga cikin wadanda suka shaida ci gaba da ayyukan.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Shugaban karamar hukumar Zuru ya gode wa Gwamna Bagudu kan rijiyoyin burtsatse Shugaban karamar hukumar Zuru ya gode wa Gwamna Bagudu kan rijiyoyin burtsatse Reviewed by on February 12, 2018 Rating: 5

ISYAKU TV

Ku dakace mu
Powered by Blogger.