Yadda jami'an NSCDC 2 suka rasa ransu wajen aiki

Wani labari da ya fito daga jihar Benue ya nuna cewa wadansu da ake zargi cewa Fulani ne sun kashe wasu jami'an tsaro na NSCDC guda biyu Mr. Adams Godwin da Abah Patrick.

Labarin ya nuna cewa an kashe jami'an ne da tsakiyar ranar Litinin a garin Awange kusa da Kessoyo a karamar hukumar Guma na jihar Benue.

Kawo yanzu dai babu tabbacin cewa Fulani ne suka kashen wadannan jami'an tsaro wadanda suka bayar da rayukansu domin kasarsu Najeriya.

An sha alakanta kashe-kashe da halaka dukiya a kan Fulani makiyaya, amma har yanzu babu hukuma da ta tabbatar da cewa Fulai ne suke aikata wannan aiki.

Idan baku manta ba, yan makonni da suka gabata a jihar Adamawa,wasu da ake zargin cewa 'yan kailar Bachama ne sun kashe tare da kone ruggagen Fulani a wani kisa na rashin imani wanda ya hada da Mata da kananan yara .

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN