Gwamna Bagudu zai kammala hanyar Jega-Koko-Yauri da tashar wutan lantarki

Gwamnan jihar Kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu ya jaddada aniyar Gwamnatinsa na inganta jin dadin rayuwar al'umman kasar Yauri da kewaye ta hanyar kammala tashar bayar da wutan lantarki na Yauri, kammala gina hanyar Jega-Koko zuwa Yauri da kuma yashe hanyoyin ruwa a wannan yankin.

Gwamna Bagudu ya shaida haka ne a fadar Mai Martaba Sarkin Yauri Alh. Dr Zayyanu Muhammad Abdullahi yayinda ya kai ziyara domin yin ta'aziyya ga Mai Martaba sakamakon hadarin jirgin ruwa da ya auku a kasar Yauri a Mako da ya gabata tare da ta'aziyya kan rasuwar Mahaifin dan Majalisar dokoki mai wakiltar Yauri Alh. Ahmad Aliyu Yauri.

Haka zalika Gwamna Bagudu ya ce zai yi kokarin ganin  cewa an kammala hanyoyin gwamnatin tarayya domin a tabbatar da an kawo sauki a rayuwar al'umma da ke amfani da wannan hanyar. Gwamnan ya ce akwai shiri na hadin guiwa tare da injiniyoyi na soji domin ganin yadda za a aiwatar da gyaran hanyar.

Mai Martaba Sarkin Yauri ya nuna rashin jindadi tare da takaici yadda wasu jami'an Gwamnatin tarayya suka yi biris da halin da hanyoyin Yauri zuwa Kontagora ke ciki.

Daga karshe Gwamana Bagudu ya ce zai biya dan kwangila mai aikin tashar wutan lantarki na Yauri Naira Miliyan 150 domin ci gaba da aikin wutan.

Daga Isyaku Garba 

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN