Wani jami'in rundunar NSCDC a jihar Sokoto ya rasa ransa yayin da yake bakin aiki sakamakon artabu da rundunar hadin gwuiwa na jami'an tsaro suka yi da wasu bata gari da suka kai farmaki a kauyen Kursa/Gobirawa a gundumar Gandi na karamar hukumar Rabah.
Safeto Nafi'u Wamakko ya rasa ransa ne yayin da rundunar hadin guiwar suke kokarin ceto wasu mutum biyu da bata garin suka yi garkuwa da su bayan sun yi gagarumar sata ranar Juma'a 19 ga Janairu.
Rahotanni sun ce barayin sun kashe mutum biyu da basu ji basu gani ba a kauyen kafin su shiga kungurmin daji da mutanen da suka sace tare da kayakin da suka sata, amma jami'an tsaron sun bi su bayan sun sami rahotu, yanayi da ya haddasa harbe harbe da bindigogi da ya kai ga halaka jami'in NSCDC Nafi'u.
Rundunar ta hadin guiwa ta hada da jami'an yansanda,soja DSS da NSCDC. Kwamandan rundunar NSCDC na jihar Sokoto Alhaji Babangida Abdullahi
Dutsinma ya ce wasu daga cikin bata garin sun tsere ne da raunukan harsashi ya kuma roki jama'a cewa su kai rahotun duk wani da suka gani da raunin bindiga ko idan basu yarda da take-takensa ba.
Tags:
LABARI