November 23, 2017

Za a kafa bataliyan zaratan sojin kundumbala a Zamfara

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayar da umarni ga soji su yi maganin 'yan ta'adda da suka addabi jama'a a cikin jihar Zamfara, wannan ya biyo bayan wani mumunar hari da 'yan bindiga suka kai ne a Shinkafi da Maradun na jihar ta Zamfara wanda ya yi sandin mutuwar akalla mutum 50 a mako da ya gabata.

Shugaba Buhari ya amince da bukatar da Ministan tsaro Brig.Gen Mansur Dan Ali (Murabus) ya gabatar masa na assasa sabon Bataliya na zaratan Sojin kundumbala a Zamfara da tabbatar da sabuwar sashen runduna ta 8 na Soji a Sokoto a bisa sabon tsarin dabarun yaki watau new Order of Battle (OBAT).

Haka zalika shugaba Buhari ya aminta da dauke Brigade na 1 daga Sokoto zuwa Gusau.

Domin tunkarar sabon salon kai hare-hare kan jama'a da kungiyar boko haram take yi ta hanyar amfani da yara kanana kuwa Shugaba Buhari ya aminta da kafa wata magama na bayanan ayyukan sirri da jami'an tsaro za su dinga yin amfani da shi domin isar da bayanan sirri a tsakanin su cikin gaggawa wadda za ta sami gindin zama a Maiduguri na jihar Borno.

Bayanai sun nuna cewa wannan lokaci za a sauya akalar yakin zuwa yaki da bayanan sirri za su jagoranta domin tunkarar 'yan ta'adda.


Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments

0 comments:

Post a Comment

Rubuta ra ayin ka

Item Reviewed: Za a kafa bataliyan zaratan sojin kundumbala a Zamfara Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
Koma Sama