• Labaran yau

  Mata ta fasa kwalba akan Miji,ta caka masa tsinin kwalba a kirji

  Wani rahotu daga jihar Zamfara ya  nuna cewa wata mata ta kwada wa mijin ta kwalba a kai ya fashe daga bisani ta daba masa tsinin kwalban a kirji da kafadarsa kuma ta bar shi a cikin jini a garin Gusau ranar Laraba.

  Bayanai sun nuna cewa an garzaya zuwa Asibiti da mutumin inda Likitoci ke kokarin ceto rayuwarsa sakamakon raunuka da ya samu .

  Wata majiya ta labarta cewa rigima ne na cikin gida da ya wuce lissafi ya zama tashin hankali.

  Wannan yana faruwa ne kwana biyu bayan wata mata ta kashe Mijinta har lahira a Maitama babban birnin tarayya Abuja.

  Haka zalika 'yan watannin baya an sami wata mata da ta kashe Mijin ta a Kaduna da Amaryarsa domin ya yi mata kishiya, bugu da kari mako uku da suka gabata wata Mace mai sun Blessing ta kashe Mijin ta a jihar Rivers bayan ta zuba masa fetur kuma ta kyasta masa ashana yayin da yake barci a kan katifa a gidan shi a birnin Portharcourt.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Mata ta fasa kwalba akan Miji,ta caka masa tsinin kwalba a kirji Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });