• Labaran yau

  'Yan sanda sun gurfanar da Maryam a kotu bisa zargin kashe Bilyamin

  Hukumar 'yansanda a Abuja ta gurfanar da Matar Marigayi Bilyamin Muhammed Bello a gaban wata babban Kotun Tarayya a birnin Abuja. Maryam Sanda wacce matar Bilyamin ce kafin rasuwarsa tana fuskantar zargin kisan Mijin ta Bilyamin a gaban Kotu da ke No.32. Jabi.
  Matar 'dan Dr. Bello Haliru ta kashe mijin ta Bilyamin sakamakon kishi
  Maryam tana fuskantar laifin zargin kisa karkashin sashe na 221 na dokokin Penal Code na Birnin Tarayya Abuja kamar yadda kakakin hukumar 'yansanda na birnin tarayya Abuja DSP Anjuguri Manzah ya sanar.
  'Yan sanda sun kama mata da masu gadi 3 na gidan marigayi Bilyamin
  Ya kuma kara da cewa wannan laifin an gurfanar da Maryam ne bisa bincike na farko, amma za'a iya sauya tuhumar idan an sami karin bayanai akan lamarin a ci gaba da bincike da hukumar take yi.
  Mata ta fasa kwalba akan Miji,ta caka masa tsinin kwalba a kirji
  Daily Post ta ruwaito cewa, tuni dai hukumar ta 'yansanda ta sami izinin tsare Maryam har sati biyu daga Kotu, amm domin Maryam tana shayar da jaririya 'yar wata shida, ba a kai ta gidan Kurkuku domin ta jira hukunci ba.

  Kakakin ya shaida wa manema labarai cewa , bisa yadda lamarin ya kasance, rundunar za ta gudanar da binciken ta da iya kwarewa kuma bisa ka'idar aikin 'dansanda.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: 'Yan sanda sun gurfanar da Maryam a kotu bisa zargin kashe Bilyamin Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });