Ma'aikatar Ilimi ta jihar Kebbi ta gudanar da taron kara wa juna sani ga Malamai 200

 Daga Nura Bena, Isyaku Garba |

MA AIKATAR ILIMI TA JIHAR KEBBI TA SHIRYA TARON KARAWA JUNA SANI GA MALAMMAI SAKANDARI  DARI BIYU 200 A FANNIIN ARABIC, I.R.K , HAUSA, P.H.E DA KUMA FRENCH.

A jawabin sa a wurin bude taron Gwamnan jihar kebbi sanata Abubakar Atiku Bagudu yace shirya irin wannan taron abu ne mai matukar muhimmaci ga alumma da ma kasa baki daya .

Gwamna Abubakar Atiku bagudu ya nuna muhimmancin ilimi a fadin Duniya tare da jaddada kudurin Gwamnatin jiha na cigaba da shirya irin wadannan tarukan da zummar shayo kan  wadansu daga matsalolin da ke sa ilimi tabarbarewa.

Sanata Atiku  ya yi kira ga malammai da suka hallara wajan karbar horon da suyi amfani da abin da suka koya a wurin taron. 

A nasu jawabai Kwamishinan ilimi na jihar kebbi Alh. Muh'd Magawata Alieru da Darakta a Maikatar ilimi ta jiha Hajiya Asma'u Alkali dukkanin su sun gode wa Maigirma gwamnan jiha Sanata Abuabakar Atiku Bagudu akan kokarin sa na bunkasa harkar ilimi a jihar nan .

Sun kuma jaddada kudurin su na ci gaba da goyon bayan su akan cigaban ilimi a jihar nan.
Masana da masu ruwa da tsaki a fannin illimi ne aka gayyato domin gabatar da kasidu a  fannin darussan.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN