• Labaran yau

  Wani Soja ya sha mugun duka a hannun 'yansanda sakamakon ojoro a ATM

  Wani Soja ya sha mugun duka a hannun wasu 'yansanda a bakin wani Banki a garin Damaturu na jihar Yobe ranar Juma'a. Bayanai sun nuna cewa takaddamar ta taso ne bayan Sojan wanda ke sanye da kakin Soja ya je ATM na wani Banki kuma ya yi kokarin zaran kudi ba tare da ya bi layi ba wanda hakan ya sa jama'a da ke cikin layin suka nuna rashin amincewa.

  Sakamakon haka yasa wani 'dansanda wanda baya cikin kaki ya kalubalanci Sojan lamari da ya kai ga tayar da jijiyoyin wuya da ya rikide zuwa dambe. Ganin haka ya sa 'yansanda da ke gadi a Bankin suka taru suka yi wa Sojan dan karen duka.

  Daily Post ta ruwaito cewa daga bisani an kira manyan jami'an tsaro inda 2i/c Mopol ya zo ya tafi da 'dansandan da aka yi dambe da shi ofishinsu yayin da wani hafsan Soja ya je ya tafi da Soja da ya daku zuwa Barikin Soja da ke Damaturu.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

   
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  Rubuta ra ayin ka

  Item Reviewed: Wani Soja ya sha mugun duka a hannun 'yansanda sakamakon ojoro a ATM Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama