• Labaran yau

  'Dan shekara 80 ya kashe Mahaifiyarsa yar shekara 100 da duka bisa zargin maita

  Rundunar 'yansanda a jihar Neja ta kama wani tsoho mai shekara 80 mai suna Kwacha Manu da 'dansa Likita mai shekara 40 bisa zargin kashe Mahaifiyarsa 'yar shekara 100 a garin Marke Gada Maje.

  Bayanai sun nuna cewa Manu ya kashe Mahaifiyarsa ce bayan ya yi zargin cewa Mahaifiyar tashi ce ta kashe jikanyarshi ami suna Magajiya 'yar shekara 17 wacce diya ce a gurin 'dan sa.

  Sakamakon haka Manu ya yi wa Mahaifiyarsa  mai suna Inno 'dan karen duka wanda ya kai ga mutuwarta .Wata majiya ta labarta cewa mazauna garin sun dade suna zargin cewa Inno tana rike kurwar mutane ta hanyar Maita da kan kai ga mutuwarsu.

  Manu ya musanta cewa da gangan ya kashe Mahaifiyarsa,ya kara da cewa shi dai yayi wa Mahaifiyarsa buloli a kafafuwanta ne yana tambayanta dalili da ya sa ta kashe Magajiya.Ya kuma ce Magajiya ta yi ta rokon Inno domin ta saki kurwar ta amma ta ki.

  Kakakin hukumar 'yansanda na jihar Neja Abigail Unaeze ya tabbatar da aukuwar lamari ya ce rundunarsa za ta gurfanar da wanda aka kama gaban Kotu.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  Rubuta ra ayin ka

  Item Reviewed: 'Dan shekara 80 ya kashe Mahaifiyarsa yar shekara 100 da duka bisa zargin maita Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama