Kwamitin fansho ya mika rahotun sa domin isarwa ga Gwamna Atiku Bagudu

 Daga Nura Bena, Isyaku Garba |

Da yake karbar rahoton daga shugaban kwamitin da Gwamnatin jihar Kebbi ta kafa kan sha'anin fansho ,  Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi Alh. Samaila Yombe Dabai ya bayyana jin dadinsa akan kokarin kwamitin na gabatar da rahoton cikin lokaci  . Tare da ba kwamitin tabbacin zai gabatar da rahotun ga Gwamnan jiha Sanata Abubakar Atiku Bagudu,domin dubawa akan aikin nasu don amincewar Gwamnati na ci gaba da biyan hakokin masu karbar fansho da garaduti .

Mataimakin Gwamnan ya kara da cewa Gwamnatin jiha za ta ci gaba da biyan hakokin wadanda suka yi ritaya da ma sauran dukkanin ma'aikatan jihar nan, ta la'akari da irin muhimmanci da kuma gudun mawar da ma aikata ke bayarwa ta hauji daban- daban, domin cigaban  jiha da ma kasa baki daya.

A jawabin sa tun farko shugaban kwamitin Alh. Muh'd kwaido, ya ce kwamitin da ya ke jagoranta yi yi kokarin kammala aikin sa ne a cikin lokaci, ta la a'kari da irin nauyin da ke ga aikin kwamitin, na tantance abin da ake ba ko ake biyan ma'aikacin da ya bar aiki watau ritaya  ko giraduti.

Alh. Muh'd kwaido yayi amfani da damar ya gode wa Gwamnatin jiha, akan irin kokari da kuma kulawar da take baiwa akan sha'anin fansho a jihar nan, ya kuma yi amfani da damar inda ya gode wa mambobin kwamitin akan irin kokari da jajircewar da suka nuna a lokacin aikin.
 
A nasu tsokaci bayan kammala gabatar da rahoton , shuwagabannin hokumomin da ke kula da biyan masu karbar fansho na kananan hukumomin na  jiha,watau (local government staff pension  board) hadi da na malaman  firamare (L.G.E.A-  Primary pension  board),Mal  Nasiru Kigo da Hajiya Nasara Yusuf duk sun nuna jin dadinsu akan kulawar gwamnatin jiha ga sha'anin fansho, tare da yin kira ga Gwamnati da ta duba da kuma yin gyare- gyaren a duk inda  ya kamata domin ci gaba da aiwatar da biyan fanshon ga dukkanin wadanda suka yi ritaya daga aiki.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN