Feshin maganin tsuntsaye a Kebbi,Gwamna Bagudu ya cancanci yabo - Samaila Yombe

Daga Nura Bena, Isyaku Garba |

An yaba wa Gwamnan jihar Kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu akan irin kokari da kuma  kulawar da yake bayarwa ga harkar feshin tsuntsayen Jan baki da sauran kwarin dake yiwa manoma da amfanin gona barazana, tare da barnata masu amfanin gona mai yawa.

Mataimakin Gwamnan jiha Alh. Samaila Yombe Dabai ne ya yi  wannan yobon a lokacin da ya ke amsa tambayoyin mane ma labarai a Arewa house dake Kaduna. 

Alh. Samaila Yombe Dabai ya ce dole ne a jijina wa mai girma Gwamnan jiha Sanata Atiku Abubakar Bagudu akan bada kulawa ta musamman na yaki da tsuntsaye a cikin lokaci. 

Mataimakin Gwamnan ya kara da cewa gwamnatin jihar kebbi, Gwamnatin talakawa ce domin a ko wane lokaci tana sauraren jama'arta,tare da biyan bukatun su, hadi da kyautawa al-umma a fanni  daban - daban na rayuwa. 

Ya kara  da cewa, bisa ga haka ne ma, kananan hukumomin jihar ke godiya ga Gwamnatin  jiha akan daukar matakan gaggawa na ceto manoman su daga barazanar tsuntsaye da sauran  amfanin gona mai tarin yawa.

Alh. Samaila Yombe Dabai, ya ce Allah ya Albarkan ci jihar kebbi da fadamar  noma da sauran wuraren  aikin  noma mai fadi,  wanda  kusan 85% na jama'ar  jihar nan manoma ne , Kuma sai gashi shugaban kasa General Muhammadu Buhari ya baiwa Gwamnan jiha shugan noman shinkafa na kasa baki daya, da manufar bunkasa tattalin arzinkin kasa da ma Afrika gaba daya.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN